Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-16 12:23:27    
Kasar Sin na goyon bayan karfafa karfin Afirka ta fuskar ciniki ta hanyar ba da tallafi

cri

Yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na Afirka a Yau. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani bayanin musamman mai lakabi haka, kasar Sin tana goyon bayan a inganta karfin Afirka a fannin ciniki ta hanyar ba da tallafi.

A gun babban taron ciniki na ba da tallafi ga kasashen Afirka da Kungiyar Ciniki ta Kasa da Kasa wato WTO ta kira a farkon wannan wata, a cikin jawabinsa, wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na nuna goyon baya kan warware matsalolin da kasashe masu tasowa ke fuskanta ta hanyar ba da tallafin fasaha, wadanda suka hada da rashin ingantaccen karfin ciniki da abubuwan da suka gaza yi a muhimman ayyukan., ta haka, kasashe masu tasowa za su sami taimako domin gudanar da yarjejeniyoyin kungiyar WTO da shiga cikin ciniki a tsakanin kasashen duniya, da kuma ci gajiyar cinikin duniya.

A gun babban taron ciniki na ba da taimako ga kasashen Afirka da aka yi a farkon wannan wata, da farko dai, Malam Yi Xiaozhun, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya yi jawabi a madadin kasar Sin, inda ya ce, saboda yana kasancewa da rashin daidaituwa a cikin tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, shi ya sa aka mai da yawan kasashe masu tasowa da suka hada da kasashen Afirka a kan matsayi 'yan rakiya a lokacin da ake raya tattalin arzikin duniya gu daya, ana bukatar canza irin wannan hali cikin gaggawa.

Ya kara da cewa, a matsayin wata kasa mai tasowa, kasasr Sin ta fahimci matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta wejan bunkasa tattalin arziki.


1 2 3