Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-05 17:32:42    
Huldar da ke tsakanin Koriya ta kudu da ta arewa ta shiga sabon zamani na sulhu da hadin gwiwa

cri
 

Yau shekaru bakwai ke nan da Roh Moo Hyun ya yi shawarwari tare da Kim Jong-Il a wannan karo, wato bayan taron shawarwarin shugabannin kasashen biyu na karo na farko. A watan Yuni na shekarar 2000, Kim Dae-Jung, wanda a lokacin ke kan kujerar shugabancin Koriya ta kudu ya kai ziyara a Koriya ta arewa, kuma kasashen biyu sun daddale "sanarwar hadin kan Koriya ta arewa da ta kudu ta ranar 15 ga watan Yuni". Daga baya kuma, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta fara kyautatuwa daga hamayya da juna har zuwa samun sulhu da kuma hadin gwiwa. Abin da ya sha bamban da yadda Kim Dae-Jung ya kai ziyara ga Koriya ta arewa cikin jirgin sama shi ne, a wannan karon, shugaba Roh Woo Hyun ya kai ziyararsa ne cikin mota, har ma ya tsallake kan iyakar kasashen biyu da kafa.

Bayan haka, abin da ya kamata a sa lura shi ne, huldar da ke tsakanin Koriya ta kudu da ta arewa ta kawo kyakkyawan tasiri ga shawarwarin da ake yi tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Koriya ta arewa. A loakcin da shugabannin kasashen Koriya ta arewa da ta kudu ke shawarwarinsu a ranar 3 ga wata, an kuma rufe shawarwarin batun nukiliyar zirin Koriya da aka yi tsakanin bangarori shida a nan birnin Beijing, inda Koriya ta arewa ta amince da lalata dukan na'urorinta na nukiliya, kuma za ta bayyana dukan na'urorin a fili kafin karshen shekarar da muke ciki. A game da wannan, mataimakin ministan harkokin waje na Sin, kuma shugaban tawagar wakilan kasar Sin a gun shawarwarin, Mr.Wu Dawei ya bayyana cewa,"wannan ba ma kawai zai amfana wa zirin Koriya da arewa maso gabashin Asiya a wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba ba, haka kuma zai taimaka wajen kyautata da kuma bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen da abin ya shafa, haka nan kuma, zai taimaka wajen samar da sabon yanayi na jituwa a arewa maso gabashin Asiya."(Lubabatu)


1 2 3