Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-05 17:32:42    
Huldar da ke tsakanin Koriya ta kudu da ta arewa ta shiga sabon zamani na sulhu da hadin gwiwa

cri

A ranar 4 ga watan nan da muke ciki, shugaba Kim Jong-il na Koriya ta Arewa tare da takwaransa na Koriya ta Kudu sun daddale "sanarwar bunkasa huldar da ke tsakanin Koriya ta Arewa da ta kudu da kuma tabbatar da zaman lafiya da albarka a tsakaninsu", wato ke nan sun kawo karshen shawarwari na yini uku a tsakaninsu. Kafofin yada labarai na Koriya ta kudu suna ganin cewa, shugabannin kasashen biyu sun cimma daidaito a wajen kafa dadadden tsarin shimfida zaman lafiya a zirin Koriya da sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arzikinsu da kuma tabbatar da samun albarka tare, kuma yana da muhimmancin gaske ta fuskar kawo sulhu da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

A ranar 4 ga wata, bayan da Kim Jong-il da Roh Moo Hyun suka rattaba hannu a kan "sanarwar bunkasa huldar da ke tsakanin Koriya ta arewa da Koriya ta kudu da kuma tabbatar da zaman lafiya da albarka a tsakaninsu", jami'an kasashen biyu sun yi tafi sosai. A gun liyafar da aka kira daga baya don yin ban kwana da shugaba Roh Moo Hyun na Koriya ta kudu, firaministan Koriya ta arewa, Kim Yong-il ya nuna amincewa ga nasarorin da aka cimma gun wannan taron shawarwarin shugabannin kasashen biyu, ya ce,"sakamakon da aka samu daga wajen wannan taron shugabannin Koriya ta arewa da ta kudu ya sake shaida cewa, dole ne za iya bude wani sabon zamani na tabbatar da albarkar al'umma, idan mun hada kanmu."


1 2 3