Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-05 15:00:28    
Murnar cika shekaru 58 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin

cri

Kasar Sin da Nigeria sun dade suna huldar diplomasiyya da kuma tattalin arziki tare, saboda haka ina kara nuna farin cikina game da kewayowar wannan rana ta 1 ga wata wanda ya kara hada kasashen tare.

Bayan haka, akwai kuma malama Fatima Ibrahim, mazauniyar garin Zaria, da ke tarayyar Nijeriya, wadda ta rubuto mana cewa, shin mene Sinawa su kan yi a ranar kasar?

To, malama Fatima, a nan kasar Sin, a kan bi hanyoyi iri daban daban domin murnar ranar kasar. Wani lokaci, a kan yi kasaitaccen biki a filin Tian'anmen da ke cibiyar birnin Beijing, babban birnin kasar Sin. A ranar da safe na ko wace shekara, dimbin jama'a da suka zo daga wurare daban daban na kasar su kan zo nan birnin Beijing, su hadu a babban filin nan na Tian'anmen, don halartar bikin daga tutar kasarsu. Bayan haka, domin murnar ranar, yanzu jama'ar kasar Sin suna da tsawon hutu na kwanaki bakwai, shi ya sa suna son zuwa wurare daban daban na kasar, har ma kasashen waje, domin yawon shakatawa.(Lubabatu)


1 2 3