Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-05 15:00:28    
Murnar cika shekaru 58 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin

cri

Ranar 1 ga watan nan da muke ciki, rana ce ta cika shekaru 58 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a kwanan nan, mun sami sakonni da yawa daga wajen masu sauraronmu, inda suka taya mu murnar ranar, kuma sakonnin sun burge mu sosai.

Malam Salisu Dawanau daga birnin Abuja, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, ko shakka babu, akwai kyakkyawar alaka da kasar Sin da Nijeriya. A kasar Sin, ranar 1 ga watan Oktoba, ranar biki ce don murnar cika shekaru 58 da aka kafa sabuwar kasar Sin. Mu a nan Nijeriya, ranar 1 ga watan Oktoba, ranar murnar cika shekaru 47 ne da samun 'yancin-kai daga Turawan Mulkin-mallaka. Da fatan za mu kara samun ci gaba da moriyar juna kamar yadda aka saba a kasashenmu biyu. Duka ina yi mana fatan alheri, da kuma karin nasarori bisa harkokinmu na yau da kullum a cikin shekaru masu zuwa. To, mun gode malam Salisu da wannan wasikar da ka turo mana, gaskiya kamar yadda ka fada, akwai kyakkyawar alaka a tsakanin Sin da Nijeriya, har ma bukukuwan murnar kafuwar kasashen biyu sun kasance cikin rana daya. Muna yi wa kasashen biyu da jama'arsu fatan alheri, kuma muna fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninsu.


1 2 3