Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-05 15:00:28    
Murnar cika shekaru 58 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin

cri

Sai kuma malam Mamane Ada daga birnin Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijer ya rubuto mana cewa, gaskiya tun ranar 28 na watan Satumba, muka samu gaiyatar jakadan kasar Sin a nan Nijar cewa da mai girma Chen Gonglai a gidansa dake nan birnin Yamai, don haka ina ganin cewa wannan rana ta 1 ga watan Oktoba 2007, wata mahimmiyar rana ce ga dukan diyan kasar Sin da kuma kasashen dake da ma'amala da wannan kasa taku, abun da ya ba ni sha'awa shi ne, samun ganawa da mai girma Chen Gonglai, na yi kuma hira da shi, na ga yadda Sinawa ke son mutanen Nijar, to abun da ya fi sosa mini rai shi ne yadda mai girma Chen Gonglai ya nuna jin dadinsa a game da huldar rediyo R&M da CRI da kuma sauraren da ake ma cri bisa FM a kan 106 a birnin Yamai, daga bisani fatan da ni ke shi ne ALLAH ya kara dankon zumunci tsakanin kasar Sin da kasar Nijar, sa'an nan ya ja zamanin huldar zamantakewar radiyo Sin da radiyo R&M. To, mun gode, malam Mamane Ada, gaskiya wannan wasikarka ta burge mu sosai, da ganin yadda huldar da ke tsakanin Sin da Nijer da kuma jama'ar kasashen biyu ke bunkasa. Bayan haka, muna fatan masu sauraronmu da ke birnin Yamai a kan 104.5 da kuma 106 za ku ci gaba da kasancewa tare da mu, ku kara fahimtar kasar Sin, da fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Sai kuma Bala Mohammed Mando daga birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, na rubuto ne domin in taya ku da dukkan jama'ar kasar Sin murnar cika shekaru 58 da kafa sabuwar kasar Sin. Wannan abin farin ciki ne sosai musamman ganin cewa ranar ta zo daidai da cikar kasar Nigeria shekaru 47 da kafuwa. Ina fatan wannan abin farin ciki zai kara dankon zumunci tsakanin kasar Sin da Nigeria, da kuma addu'ar karuwar habakar arzikin kasashen da kuma zaman lafiya mai dorewa.


1 2 3