Abin da ya fi jawo hankulan mutane shi ne, bisa hanyarsa zuwa birnin Pyongyang, Mr. Roh Moo Hyun kuma zai sauka daga mota, zai ketare layin iyakar soja da kafafuwansa zuwa gefen Korea ta arewa. A ran 30 ga watan Satumba, Mr. Lee Jae Joung, ministan dinkuwar kasa ta Korea ta kudu ya bayyana cewa, ketare bakin iyakar kasa wajen sha'anin soja da shugaban kasar Korea ta kudu ya yi da kafafuwansa zai zama wani lokaci mai faranta ran mutane kuma mai ma'anar tarihi, muna fatan wannan matakin da aka dauka zai jawo kyayyawan yanayi mai na'anar tarihi domin tabbatar da zamna lafiya a zirin Korea.
Ra'ayoyin Korea ta kudu sun bayyana cewa, Korea ta arewa ta nuna "amincewa da sassauci" wadanda suka sha bamban da na da cikin ayyukan share fage da ta yi domin wannan shawarwarin shugabannin. Ba ma kawai ta yarda da kungiyar wakilan Korea ta kudu da ta ziyarci Korea ta arewa ta hanyar motoci ba, kuma ta yarda da Korea ta kudu da ta yi amfani da motocinta don watsa wasu aikace-aikacen da hukumar Korea ta kudu ke yi a Korea ta arewa ta hanyar telebijin kai tsaye, kuma ta samar wa kungiyar wakilan Korea ta kudu wayar salula 30 da hanyoyin sadarwa 12. 1 2 3
|