Bayan shekaru 7 da aka yi ana shawarwari a karo na farko tsakanin shugabannin kasashen Korea ta kudu da ta arewa, ga shi kuma banganrorin 2 sun sake yin shawarwari tsakanin shugabanninsu. A ran 5 ga watan Agusta na wannna shekara, Korea ta kudu da ta arewa sun bayar da "Yarjejeniyar tsakanin kudu da arewa" a sa'i daya dangane da shawarwarin da za a yi a birnin Pyongyang a tsakanin shugaba Roh Moo Hyun na Korea ta kudu da shugaba Kim Jong Il na Korea ta arewa. Yarjejeniyar ta bayyana cewa, bisa harsashen tattara sakamakon da bangarorin 2 suka samu cikin shekaru 7 da suka wuce wajen samun sulhuntawar al'umma da yin hadin gwiwa tsakaninsu, za su tattauna matsalolin kara amincewa juna da kafa tsarin shimfida zaman lafiya a zirin Korea, da kuma kyautata hadin gwiwa a tsakaninsu wajen tattalin arziki.
Bayan da Korea ta kudu da ta arewa suka yi shalar yin shawarwarin karo na 2 a tsakanin shugabanninsu, bangarorin 2 kuma sun yi shawarwari sau da dama a tsakaninsu, har sun samu ra'ayi daya kan jadawalin shawarwarin shugabanninsu da yawan mutanen kungiyar wakilan kasar Korea ta kudu, da hanyar da kungiyar za ta bi wajen yin ziyara.
1 2 3
|