Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-01 18:00:04    
Za a sake yin shawarwari tsakanin shugabannin kasashen Korea ta kudu da ta arewa

cri

Daga ran 2 zuwa ran 4 ga watan Oktoba a birnin Pyongyang, za a yi shawarwari na karo na 2 tsakanin shugabannin kasashen Korea ta kudu da ta arewa. A ran 2 ga wata kuma shugaba Roh Noo Hyun na Korea ta kudu ya tashi daga birnin Seoul cikin mota ta musamman ya bi ta hanyar motoci da ta hada birnin Seoul da jihar Sinui ju ta Korea ta arewa don zuwa birnin Pyongyang, inda zai yi shawarwari da Mr. Kim Jong Il, shugaban kasar Korea ta arewa. Ra'ayoyin jama'a sun bayyana cewa, wannan shawarwarin zai sa kaimi ga ci gaban dangantakar da ke tsakanin bangarorin 2, kuma za a bude wani sabon shafi ful wajen halin da ake ciki a zirin Korea.

A watan Yuni na shekarar 2000, an yi shawarwari na karo na farko tsakanin shugabannin kasashen Korea ta kudu da ta arewa, wanda ya bude wani sabon shafi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen 2. Da ga nan ne Korea ta kudu da ta arewa suka kauce wa hanyar da suka bi a lokacin yin yakin cacar baki da yin adawa da juna, kuma sun shiga cikin zamanin samun sulhu da yin hadin gwiwa a tsakaninsu.


1 2 3