Manazarta suna ganin cewa, dalilin da ya sa babban wa ya fi basira shi ne sabo da yana iya samun albarkatun gida da yawa, kuma yana daukar alhakin koyar da kannensa maza da mata, ban da wannan kuma iyayensa su kan sa rai sosai gare shi.
Dr. Kirstense ya bayyana cewa, albarkatun kara basira da kuma abubuwan kara kwarin gwiwa da yara suka samu daga iyayensu suna takawa muhimmiyar rawa garesu.
Bugu da kari kuma Dr. Kirstense ya gano cewa, a cikin karamin gida, bambancin da ke tsakanin babban wa da kane wajen bisira yana nan a bayyane, amma idan tazarar shekaru tsakaninsu ta yi yawa, to ba za a kansace da wannan bambanci ba.
Haka kuma Dr. Kirstense ya ce, zai mai da hankali kan 'yan uwa da ke cikin wani gida da ke kasancewa da al'adu iri daban daban, wanda za a iya samu membobi gida da yawa.(Kande) 1 2 3
|