Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-26 14:56:44    
Wa ya fi kane basira

cri

Dr. Kirstensen da abokan aikinsa sun gudanar da bincike ga maza dubu 240 na kasar Norway, daga baya kuma sun gano cewa, a cikin wani gida, matsakaiciyar jimlar basira wato IQ ta babban wa ta fi ta kane na biyu yawa har kashi 2.3 cikin dari, kuma wannan jimla ta kane na biyu ta fi ta kane na uku yawa har kashi 1.1 cikin dari.

Wani namiji ko shi ne babban wa, ko kane na biyu, ko kuma kane na uku, idan an ciyar da shi a matsayin babban wa, to ya fi basira. Dr. Kirstense ya bayyana cewa, wannan nazari ya shaida cewa, matsayi na wani mutum a gida yana taka muhimmiyar rawa ga basirarsa a maimakon odar haihuwa.

Ban da wannan kuma rahoton nazarinsu ya shaida wani ra'ayin da masu ilmin kimiyya da yawa suke shakka a cikin shekaru fiye da dari da suka gabata, wato babban wa yana da rinjaye.

Amma bayan da aka bayar da wannan sakamako, an yin muhawara a kansa, dalilin ya sa haka shi ne sabo da yanayin ko wane gida ya sha bamban. Yin la'akari kan wannan batu, Dr. Kirstense da kungiyarta sun gudanar da bincike kan 'yan uwa da ake ciyar da su a cikin gida guda.


1 2 3