Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-26 14:55:08    
Wani dan sanda mawallafi mai suna Cao Naiqian

cri

Yanzu, Mr Cao Naiqian yana nan yana wallafa wani labari dangane da mahaifiyarsa, kuma yawan kalmomin da ya wallafa sun riga sun kai dubu 200, ya yi shirin kammala rubuce-rubucen a shekara mai zuwa, wannan burinsa ne tun daga dogon lokaci na da, mahaifiyarsa ta taba kamuwa da ciwon tabin hankali, ba ta iya kula da ita kanta ba, don kula da mahaifiyarsa sosai da sosai, sai Mr Cao Naiqian bai wallafa kowane labari ba, bayan rasuwar mahaifiyarsa, ya yi bakin ciki sosai, yana son waiwayi abubuwan da mahaifiyarsa ta yi a lokacin da take da rai a duniya da kuma nuna godiya ga mahaifiyarsa bisa gudumuwar da ta yi. Ya ce, na riga na yi rubuce-rubucen a shekara daya da rabi, yawan kalmomin da na rubuta ya kai dubu 200, bisa kimantawar da na yi,an ce, yawan kalmomin da zan rubuta a cikin labarin zai kai dubu 400 zuwa 500, wasu mutane sun ce, abin da na rubuta na da tsawo sosai, kuma sun shawo kaina cewa, kada na rubuta labarin da tsawon haka, amma ban lura da abin da suka fada ba, a gani na, abin da na rubuta yana shafar mahaifiyata, kodayake na da tsawo sosai, watakila ba za a iya buga shi ba, amma na tabbatar da cewa,dole ne na kammala rubuce-rubucen don biyan burina na tunawa da mahaifiyarta.

A gaskiya dai ni ne wani mai rowa, ba na son sayen abubuwa da yawa domin ni kaina wajen zaman rayuwa, amma ina son sayen litattafai da yawa ko da arha ko da tsada, a cikin karamin gidana , a ko'ina da akwai littattafai da na sayi, yawansu ya kai dubu 4 zuwa dubu 5.(Halima)


1 2 3