Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-26 14:55:08    
Wani dan sanda mawallafi mai suna Cao Naiqian

cri

A shekarar 1987, Mr Cao Naiqian ya soma wallafa labarai wadanda yawan kalmominsu ya kai miliyoyi. Mr Cao Naiqian ya bayyana cewa, ya zama wani mawallafi bisa sakamakon cacar baki da ya yi da wani amininsa. Amininsa ya ce, ba zai zama mawallafi har abada ba, amma shi kansa bai amince da maganarsa ba, ya yi ta kokarin wallafa labarai ga jaridun lardinsa, sa'anan kuma an bayar da wasunsu. Sa'anan kuma ya bayar da wasu abubuwan da ya wallafa a wasu jaridu da mujallu na Beijing da sauran wurare, wani mashahurin mawallafi ya gano shi, kuma yana son labaran da ya wallafa, ya yi kokarin horar da shi, saboda haka ya soma zaman rayuwarsa na yin wallafe-wallafe.

Labarin farko da ya wallafa yana shafar abubuwan da suka faru a tsakaninsa da wani mai bin addinin Buddah, Mr Cao ya ce, lokacin da na cika shekaru 9 da haihuwa, na taba zama tare da mabiyan addinin Buddah a cikin wani haikalin Buddah, saboda haka abubuwa dangane da addinin Buddah sun ba da tasiri sosai gare ni, shi ya sa yawancinsu da na wallafa sun shafi addinin Buddah.

Yanzu, Mr Cao Naiqian ya riga ya fitar da littattafansa na dogo da na gajeru da yawa, ya wallafa dukansu ne bisa zaman rayuwarsa, kafin da ya zama dan sanda, ya taba zama wani ma'aikacin haka kwal, a wancan lokaci, ya yi ta fama da mawuyacin hali da talauci, wani littafin da ya wallafa ya bayyana mawuyacin halin da masu haka kwal suke ciki da tsayayyar niyyarsu. Wani littafi daban da ya wallafa a shekarar da muke ciki, ya bayyana yadda masu haka kwal suke fama da talauci da mawuyacin halin da suke ciki, ya ce,in babu hakikanan abubuwan da na dandana ba, to ban iya wallafa irin wannan littafi dangane da zaman rayuwar manoma da ke fama da talauci sosai ba.ya ce, dukkan labaran da na wallafa suna fito ne bisa hakikanan abubuwan da aka yi, kuma na fahimce su sosai da sosai , in ban sami hakikanan abubuwan da aka yi a cikin zaman rayuwa ba, to ba zan wallafa labarai ba. Abubuwan da na wallafa dukkansu da suka faru ne a zaman rayuwata kuma na taba ganinsu da idona.


1 2 3