Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-26 14:55:08    
Wani dan sanda mawallafi mai suna Cao Naiqian

cri

Cao Naiqian da ke da shekaru 59 da haihuwa shi ne wani dan sanda na birnin Datong na lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin. Bambancin da ya samu da na sauran 'yan sanda shi ne , mashahurin dan sanda mawallafi ne gare shi. An fassara kuma an bayar da littattafan da ya wallafa dangane da gajerun labarai da yawansu ya kai 30 ko fiye zuwa kasar Japan da Amurka da Canada da sauran kasashe. Mun sami labari cewa, Mr Ma Yueran mai ba da sharhi wajen bayar da lambar yabo ta Nobel yana ganin cewa, yana daya daga cikin wadanda za su sa ran alheri ga samun lambar yabo ta Nobel na kasar Sin.

An haifi Mr Cao Naiqian a kauyen Xiamayu na gundumar Ying ta lardin Shanxi. A shekaru 60 zuwa 70 na karnin da ya wuce, ya taba zama ma'aikacin haka kwal da dan wasan nuna fasahar kide-kide na kungiyar nuna wasannin fasahohi , amma daga baya ya zama wani dan sanda.


1 2 3