Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-26 10:14:51    
Kasar Sin ta yi lale marhabin da karbar wutar yula mai tsarki ta taron wasannin Olympic na musamman

cri

An yi raye-raye da wake-wake masu ban sha'awa kafin a yi bikin kunna wutar yula, nan take mutane sama da 100 na gida da na waje suka shiga cikin wurin taron rike da wutar yula. Mr. Wu Guanzheng, wakilin din-din-din na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma sakataren kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar ya karbi wutar yula ya kuma kunna ta, sai halin fara'a ya game duk wurin taron. Daga baya dai Mr. Wu ya yi shelar soma mika yula a yankin kasar Sin. " Yanzu bari in yi shelar mika wutar yula ta taron wasannnin Olympic na musamman na duniya na lokacin zafi na shekarar 2007 cikin yankin kasar Sin".

Wasannin Olympic na musamman, wasanni ne da aka shirya musamman domin mutane masu tabin hankali. Akan gudanar da irin wannan taron wasannin sau daya cikin shekaru biyu-biyu. An raba wannan taron wasanni na lokacin zafi da na sanyi. Za a gudanar da irin wannan gagarumin taron wasanni na 12 a birnin Shanghai na kasar Sin. Wannan ne karo na farko da za a gudanar da shi a wata kasa ta Asiya wadda kuma kasa ce mai tasowa. An labarta cewa, akwai 'yan wasa da masu koyar da 'yan wasa, da iyayen 'yan wasa da kuma kwararru da dai gaggan baki su fiye da 20,000 da za su halarci taron wasannin. Gwamnatin kasar Sin da kuma birnin Shanghai sun yi matukar kokari wajen shirya wannan taron wasanni. A gun bikin kunna wutar yula, mataimakin firaministan kasar Sin Mr. Hui Liangyu ya furta cewa : ' yanzu kasar Sin na da nakasassu da yawansu ya kai miliyan tamanin da biyu da dubu dari tara da sittin, ciki har da mutane masu tabin hankali da yawansu ya wuce miliyan tara da dubu dari tara. Gwmnatin kasar na mai da hankalinta sosai kan ayyukan nakasassu, wato ke nan takan nuna goyon baya ga bunkasa sha'anin nakasassu da kuma kawar da wahalhalun dake gaban nakasassu masu tarin yawa ciki har da mutane masu tabin hankali a fannin samun magani da ilmi da kuma aikin yi. Manyan nasarorin da kasarmuta samu a fannin yalwata sha'anin nakasassu sun samu amincewa da kuma yabo daga gamayyar kasa da kasa.


1 2 3