Zane-zanen takarda na gargajiya da aka yanke sun yi farin jini sosai a tsakanin Sinawa, sa'an nan kuma, masu yawon shakatawa na waje sun mayar da su tamkar kayan fasaha. An taba bai wa tsohon shugaba Jacques Chirac na kasar Faransa zanen takarda na zakara da madam Zhao ta yi da hannu tamkar abin kyauta daga gwamnatin kasar Sin.
Yanzu shagon Baigongfang ya riga ya zama muhimmin wuri ne da gwamnatin kasar Sin ke karbar baki na kasashen waje. A ran 8 ga watan Maris na shekarar 2005, matan jakadun kasashen Amurka da Jamus da Cuba da Afirka ta Kudu da Armenia da kuma Kungiyar Tarayyar Turai a kasar Sin da sauran kasashe da yankunan duniya fiye da 40 a kasar Sin sun kawo wa wannan shahararren shago da ke nan Beijing ziyara, inda suka ji dadin kallon nagartattun fasahohin wadannan kwararre masu ilmin fasaha, sun kuma sami kayayyakin fasaha tamkar abin kyauta, wadanda aka yi a shagon.
Malam Tao Ye ya yi bayanin cewa, masu yawon shakatawa na iya kara fahimtarsu kan fasahohin gargajiya na kasar Sin ta hanyar zayyana da kuma kera kyayayyakin fasaha da kansu. Yana ganin cewa, ya kamata shagon Baigongfang zai kara nuna wa kasashen duniya kayayaykin fasaha na gargajiya na kasar Sin da kuma tarihinsu a nan gaba. ya ce, 'Shagon na kiyaye fasahohin gargajiya na kera kayayyakin fasaha da hannu na Beijing ko kuma na kasar Sin, wadanda suke bakin bacewa, a sa'i daya kuma, ya karbi sauran kwararru a sauran muhimman fannoni, ta haka shagon ya zama wani dandalin nuna fasahohin gargajiya na kasar Sin.'(Tasallah) 1 2 3
|