Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-25 15:48:40    
Akwai wani shagon sayar da kayayyakin fasaha da aka yi da hannu a nan Beijing (2)

cri

Baya ga irin wannan kwarya ta musamman, fasahar yanke takarda da almakashi na daya daga cikin fasahohin gargajiya na kasasr Sin. An ce, irin wannan fasaha ta bullo ne a karni na 6 bayan haihuwa Annabi Isa A. S.. A can da an yi amfani da zane-zanen takarda da aka yanke da almakashi a gun bukukuwan addinai, amma yanzu an yi amfani da su tamkar kayan ado. Madam Zhao Caixuan tana aiki a karamin shagon sayar da zane-zanen takarda da aka yanke da almakashi a cikin shagon Baigongfang. Dukkan yaranta da kuma jikanta da ita 5 na iya yin zane-zane da kuma yanke takardu, ma iya cewa, iyalinta iyali ne masu fasahar yanke takarda na ainihi. Ta yi karin bayanin cewa, (??2,?)

'A can da fararen hula sun yi amfani da takardu a maimakon gilas, in lokacin kaka ya yi, sun shafa tagogi da takardu, amma kada su yi amfani da fararen takardu, shi ya sa sun yanke wasu zane-zanen takardu, sun hada su a kan tagogin. In wata namiji ya auri wata budurwa, kada a yi amfani da fararen takardu wajen shafa tagogin dakinsu, shi ya sa an yanke wasu zane-zanen takarda. In wata budurwa ta iya irin wannan fasaha, to, za ta sami karbuwa sosai a tsakanin mutanen garinta.'

Madam Zhao ta ci gaba da cewa, fararen hula na kasar Sin sun yanke zane-zanen takarda ne domin kyautata kyan ganin zaman rayuwarsu, shi ya sa zane-zanen da mutanen arewacin kasar Sin da na kudancin kasar Sin suka yanke na sha bamban da juna sosai saboda wuraren da suke zama.


1 2 3