Bayan shiga babbar kofar shagon Baigongfang, inda ake sayar da kayayyakin fasaha da aka yi da hannu, wani karamin shago tare da rataya kore da yawa a kofarsa ya jawo hankulan mutane sosai, shi ne shagon sayar da kore. Ana ajiye kore manya da kanana masu siffofi daban daban a ko ina a cikin wannan shago. Mai shagon malam Ji Shun yana zaune a gaban teburinsa, ya yi wa maziyarta karin bayani kan koren da ya yi zane-zane ta hanyar kona a kansu, a yayin da yake kona zane-zane a kan wata kwarya, ya ce,
'A can da, saboda babu wutar lantarki, shi ya sa masu fasahar kona zane-zane kan kore sun yi amfani da wuta, a wani lokaci ma, an ajiye sandunan karfe siriri a cikin wuta, daga baya, an yi amfani da su wajen kona zane-zane a kan fuskokin kore. Yanzu an yi amfani da wutar lantarki wajen kona zane-zanen kan fuskokin kore.'
Masu kananan sana'o'i na kan kona zane-zanen furanni da tsuntsaye da kifaye da kuma tsutsotsi a kan kore, wadannan zane-zane na da kyan gani, haka kuma su alamu ne da ke kawo kyakkyawan fatan alheri, shi ya sa masu yawon shakatawa na gida da na ketare na kan nuna sha'awa sosai kan wadannan kyawawan kore. Masu fasahar kona zane-zane a kan kore da ke aiki a wannan shago sun sabunta irin wannan fasaha da kansu bisa tushen koyon wannan tsohuwar fasaha. Masu sauraro, in ku kai ziyara a wannan shago, ba kawai za ku iya more idanunku da koren da kwararru suka kona kyawawan zane-zane a kan fuskokinsu da kuma sauran kayayyakin fasaha na kore ba, har ma za ku iya samun damar kona zane-zane a kan kore da kanku, ba safai ku kan sami irin wannan dama mai daraja ba.
1 2 3
|