Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-24 14:59:12    
Shiyyar tattalin arziki ta birane uku na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin

cri

Biranen nan uku suna taimakon juna wajen bunkasa harkokin tattalin arzikinsu. Yanzu, shiyyar tattalin arziki ta biranen uku tana ta kara taka rawa wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin duk jihar Mongoliya ta gida. Malam Han Zhiran, sakataren reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a birnin Hohhot ya bayyana cewa, "na daya, garuruwa da gundumomi wadanda ke zagayen shiyyar tattalin arziki ta biranen nan uku suna cin gajiyar ci gaban shiyyar wajen bunkasa tattalin arzikinsu. Na biyu, kwararrun shiyyar suna ba da babban taimakonsu wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin wurare da ke zagayen shiyyar a fannin fasaha da sufuri da sauransu. Na uku, a sakamakon bunkasuwa da take samu, shiyyar tana kara daukar 'yan kwadago daga wurare da ke zagayenta."

Bisa ci gaba da ake samu a shiyyar, jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin ta bunkasa harkokin tattalin arzikinta cikin sauri a 'yan shekarun nan da suka wuce. Ba ma kawai ci gaba da aka samu a shiyyar ya gwada wani misali ga bunkasuwar tattalin arzikin jihar Mongoliya ta gida a cikin shekaru 60 da suka wuce tun bayan kafuwarta ba, har ma zai ba da babban taimako ga jihar wajen kara bunkasa tattalin arzikin jihar cikin sauri.(Halilu)


1 2 3