Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-24 14:59:12    
Shiyyar tattalin arziki ta birane uku na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin

cri

Abin da tsohon ke nufi shi ne a farkon lokacin kafuwarta, jihar Mongoliya ta gida tana da kananan wuraren aikin hannu da ke samar da shayi da zawati da gishiri da kuma sukari, kiwon dabbobi kuma babbar sana'a ce ga jama'ar jihar nan. Bayan kafuwar jihar, musamman tun daga farkon shekaru 1970, an gabatar da shawara kan bunkasuwar wurare masu rinjaye, wadanda suka hada da birarnen Hohhot da Baotou da kuma E'erduosi. Wadannan birane uku suna makwabtaka da juna, kuma suna da albarkatun kasa kamar kwal da ma'adinan karfe da sauransu. Sabo da haka suna kan matsayi mai rinjaye wajen kafa shiyyar bunkasa tattalin arzikin birane.

Birnin Baotou babban birnin masana'antu ne a jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar harkokin kanta. Malam Wang Huiming, shugaban hukumar kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya ta birnin ya bayyana cewa, "muna kara samar da kayayyaki masu dimbin yawa ta hanyar yin kwaskwarima kan masana'antun gargajiya,, ta haka za mu daga ingancin kayayyakin. Wannan wani tushe ne ga samun bunkasuwa cikin sauri a birninmu na Baotou."


1 2 3