Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-24 14:59:12    
Shiyyar tattalin arziki ta birane uku na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin

cri

Birane uku kamar Hohhot da Baotou da E'erduosi suna yamma maso tsakiyar jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin. Yawan kudi da aka samu a biranen uku daga wajen samar da kayayyaki wato GDP ya wuce rabi na duk jihar a shekarar bara. Yanzu, biranen uku sun riga sun zama shiyyar da ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar cikin sauri.

Jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kafu a ran 1 ga watan Mayu na shekarar 1947, kuma ita ce jihar kananan kabilu mai ikon tafiyar da harkokin kanta da aka kafa tun da wuri a kasar Sin. A farkon lokacin kafuwarta, yawan mutanen jihar makiyaya ne, jihar kuma tana koma baya sosai wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma. A cikin shekaru 60 da suka wuce, bisa babban taimako da gwamnatin kasar Sin ta bayar da kuma kokarin da jama'ar kabilu daban daban na jihar suka yi ne, yanzu, jihar ta sami ci gaba wajen bunkasa harkokin tattalin arziki cikin sauri. Wani tsoho mai suna Keli, dan kabilar Mongoliya mai shekaru 92 da haihuwa a bana ya ganan ma idonsa bunkasuwar tattalin arzikin jihar. Ya ce, "wata karin magana da ake alamanta tattalin arzikin jihar Mongoliya ta gida da shi a da, ita ce a samar da shayi da zawati da ruwa da gishiri da sukari, da kiwon rakuma da shanu da dawaki da kuma awaki kawai a jihar."


1 2 3