Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-19 15:56:26    
An bude babban taron majalisar dinkin duniya na karo na 62 a birnin New York

cri

A takaice dai, batutuwan da za a tattauna a gun babban taron nan na majalisar dinkin duniya da tarurrukan manyan jami'ai da za a yi sun kasu cikin kashi biyu, wato batututuwa masu tsanani na yankunan duniya da batutuwan yin kwaskwarima kan majalisar. Batutuwan da za a tattauna a gun babban taron nan sun kai 160, sun shafi manyan fannoni 9 kamar na zaman lafiya da tsaro da ci gaba da hakkin dan adam da kwance damara da yaki da ta'addanci da gyare-gyaren tsarin shugabancin majalisar da sauransu. Mr Srgjan Kerim, sabon shugaban babban taron majalisar ya tsai da manyan ayyukan da wannan babban taron majalisar ke yi a fannoni biyar na sauyawar yanayi, da samun ci gaba da tattarawar kudade, da manufar samun bunkasuwa ta shekaru 1000, da sa kaimi ga shirya yaejejeniyar yaki da ta'addanci, da kuma yin kwaskwarima kan tsarin kulawa na majalsiar dinkin duniya. Yana fatan za a sami ci gaba sosai wajen yin wadannan ayyuka ta hanyar kokarin da babban taron zai yi a cikin shekara daya da yake zama shugaban babban taron.

Akwai wani batun da ya cancanci a lura da shi a gun babban taron majalisar shi ne batun na wai "shigar da Taiwan cikin majalisar dinkin duniya". Wannan karo na 15 da Taiwan ya tunzura wai kasashe da ke da "dangantakar diplomasiya" da su gabatar da shirin batu kan shigar da Taiwan cikin majalisar, kuma a karo na farko an yi tambayar neman shigar da ita cikin majalisar bisa sunan Taiwan. Za a tattauna shirin batun a gun taron hukumar kula da harkokin babban taron majalisar dinkin duniya da za a yi a ran 19 ga wannan wata. Amma 'yan diplomasiya suna ganin cewa, shirin batun neman shigar da Taiwan cikin majalisar dinkin duniya zai sake bin ruwa daidai kamar yadda ya yi a da.

Tun daga ran 25 ga wannan wata, za a shafe mako daya ana yin babbar muhawara a gun babban taron nan. Malam Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin zai hallarci babban taron da babbar muhawara tun daga ran 23 zuwa ran 29 ga wannan wata. (Halilu)


1 2 3