Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-19 15:56:26    
An bude babban taron majalisar dinkin duniya na karo na 62 a birnin New York

cri

Ran 18 ga wannan wata da maraice, an bude babban taron majalisar dinkin duniya na karo na 62 a birnin New York, wakilai da suka fito daga kasashe daban daban sun halarci taron shekara-shekara da majalisar dinkin duniya ta shirya a babban zaunenta, don musanya ra'ayoyi da tattauna kan batutuwa da ke jawo hankulansu duka.

Idan an kwatanta taron shekarar nan da na shekarun baya, za a samu abubuwan musamman biyu, wato su ne, na daya, manyan jami'ai na halartar taron, na biyu, sauran tarurukan da ake yi a tsakanin manyan jama'ai na bangarori da dama sun yi yawa.

An ruwaito cewa, shugabannin kasashe ko na gwamnatoci na sama da rabin mambobin majalisar na halartar taron wannan shekara. Daga cikinsu, akwai shugabannin kasashe 76 da shugabannin gwamnatoci 32 da kuma mataimakan shugabannin kasashe 14. Ta haka taron ya zama taron da ya fi samun manyan jami'ai, tun bayan da majalisar ta kira taron koli don murnar ranar cika shekaru 60 da kafa ta a shekarar 2005.


1 2 3