Bisa binciken da aka yi, an ce, babban dalilin da ya sa shugabannin kasashe da na gwamnatoci da yawa kamar haka suke halartar taron shekarar nan, shi ne domin kasashe da ke mai da hankali ga yin amfani da dandalin majalisar dinkin duniya wajen yin harkokin waje a tsakanin bangarori da dama sai kara karuwa suke yi.
Wani dalilin daban da ya sa haka shi ne domin rawar da Ban Ki-moon, babban sakataren majalisar ke takawa. Tun bayan da ya zama babban sakataren majalisar a farkon shekarar nan, ya yi kokari sosai wajen sa kaimi ga daidaita batutuwan gaggawa iiri daban daban a duniyar yanzu. A karkashin jagorancinsa kai tsaye, za a kira tarurrukan manyan jami'ai da dama a lokacin babban taron nan wadanda suka hada da taron manyan jami'ai na karo na biyu kan batun Darfur na kasar Sudan da taron sauye-sauyen yanayi da sauransu. Haka kuma a lokacin babban taron, za a shirya tarurrukan manyan jami'ai da yawa a kan batutuwan Iraki da Afghanistan da gabas ta tsakiya da Afrika da Kosovo da sauransu, sa'an nan za a shirya tarurrukan manyan jami'ai a kan harkokin samun ci gaba da tattara kudade da kuma a tsakanin al'adu da addinai daban daban.
1 2 3
|