Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-13 19:10:21    
Bayani kan kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing

cri
 

Kan ayyukan ba da hidima,sashen kula da kayayyaki,sashe ne na ba da guzuri na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing,ya dau nauyin samar da hidima ga sauran sassa.Gagarumin wasannin Olympics na Beijing na bukatar kayayyaki masu dimbin yawan gaske da suka shafi gasa da kiwon lafiya da yada labarai da kuma kula da filayen gasa.Sashen kula da kayayyaki ya dau nauyin saye wadannan kayayyakin da ake bukata da tanadinsu da aikawa da su da kula da su.Kafin wasanni ya kamata a tanadi kayayyaki,sannan a kai wasu zuwa sassan da suke bukata,a lokacin yin wasanni,sassa da dama suna bukatar sashen kula da kayayyakin.Mr Sheng Jingyu,wani ma'aikacin sashen kula da kayayyaki ya yi mna bayani kan ayyukansu.

"Ya kamata masu kula da aikin bayar da lambobi su shirya tutocin mulkin kasa da lambobin girmamawa da kuma dandali da sanar da sashen kula da rediyo da ya shirya wakar mulkin kasa kafin a ba da lambobin girmamawa ga 'yan wasa bayan da aka gama wata gasa nan take.ma'aikatan da suka shiga wannan aiki kai tsaye sun kai wajen talatin."

Dukkan sassa na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing sun dora muhimmanci kan ayyukansu filla filla da nema kammala su yadda ya kamata.Sun mayar da hankulansu sosai wajen tsara fasalin Olympic Village wanda ya ba da hidima ga 'yan wasa da jami'ai 16,000 kan dakunan kwana da zama da shakatarwa da kuma nishadi.Mr Wu Jingbo,mataimakin shugaban sashen kula da olympic Village na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya yi bayani kan tsara fasalin dakunan kwana.Ya ce,

"Da farko mun mai da 'yan wasa a gaban kome,gadon da muka shirya don dan wasa ya fi fadi,mun kuma kara wata kujera a ciki,ta haka dan wasa na iya yi barci mai kyau sosai.ga 'Yan wasa nakasassu,mun mai da hankali sosai kan kowane kayan da suke amfani da su a cikin dakunan kwana ko akwatin ajiye tufafi ko aljihun tebur duk domin kawo musu sauki."Wani ma'aikaci na sashen kula da Olympic village ya gaya wa wakilinmu cewa a cikin ko wane dakin kwana,an manna wani zanen da yara suka zana kan jikin bango inda kananan yara na kasar Sin suka bayyana surar wasannin Olympics na Beijing a zukatansu.Zane zanen da yara suka zana sun kayatar da dakunan kwana,kuma kyautoci ne na musamman da aka kawo wa baki da suka kwana cikin dakunan.

Ko ina ana iya jin kulawa da ake nunawa a sashen kula da wasannin Olympic na nakasassu na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing.Kwamitin ne shi ma ya dau nauyin shirya wasannin Olympics na nakasassu.wannan karo na farko a cikin tarihin shirya wasannin Olympic a duniya.(Ali)


1 2 3