Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-13 19:10:21    
Bayani kan kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing

cri

Lokacin fara wasannin Olympics na Beijing na shekara ta 2008 ya kusanto mana,a kan matsayin shirya wannan wasannin Olympics na Beijing,ta yaya kwamitin shiryar ya gudanar da ayyukansa na share fage.To,a cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani kan kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing.

A ran 13 ga watan Disamba na shekara ta 2001 ne aka kafa kwamitin shirya wasannin Olympics na 29,nauyin dake bisa wuyansa shi ne shirya wasannin Olympics na Beijing da da wasannin nakasassu na Beijing.Kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing yana da sassa 24,ciki har da sassan kula da harkokin hukuma,da cudanya da kasashen ketare,da wasanni da yada labarai da kuma fadakar da jama'a,da mika sandunan tocila da rajista da sayar da takardun shiga wuraren wasanni..Tare da cigaban ayyukan share fage na wasannin Olympics na Beijing,an kara sassa na kwamitin shiryar.Har zuwa lokacin fara wasannin Olympics na shekara ta 2008,sassan kwamitin zai wuce talatin.

Sanin kowa ne muhimmin aikin wasanni shi ne gasa,dukkan ayyuka da ake yi domin tsara jadawalin gasa.Da ya ke wannan jadawalin gasa,karamin littafi ne,ma'aikata sama da dari na sashen kula da wasanni sun dukufa sau da kafa kan wannan aiki.Mr Liu Wenbing,shugaban sashen kula da wasannin kwamitin shirya naBeijing ya bayyana cewa,

"Da farko abu mafi muhimmanci shi ne,mun yi iyakacin kokarinmu na samar da kyakyawan sharuda ga 'yan wasa ta yadda za su iya kago matsayin koli a cikin gasa tare da la'akari da sassan da abin ya shafa,kamar su hadaddiyar kungiyar wasa daban daban ta duniya da harkokin gidajen rediyo mai hoto na aika da labarai.Na farko mu tsara jadawalin gasa na ko wace rana,kamata ya yi mu yi shi filla filla.Alal misali,gudun mita dari na maza,an kasa shi zuwa kungiyoyi nawa da rukunoni nawa da wace rana da karfe nawa za a yi gudu.Lalle babban aiki ne."


1 2 3