Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-13 19:10:21    
Bayani kan kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing

cri

Aikin ya yi wa sashen nan yawan gaske,ma'aikatan sashe ma na karuwa.Ma'aikatan dake kula da wasa daya kawai sun kai wjen 800.A lokacin wasannin Olympics,sashen kula da wasanni zai dauki masu sa kai kwararru ko ba kawararru sosai ba dubu goma.

Mr Zhang Yanpeng,wani dan sa kai dake aiki a sashen kula da wasanni na kwamitin.Ya ce 'yan sa kai sun shiga ayyuka da dama na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing.Babban aikinsa a yanzu shi ne amsa tambayoyin da aka kawo ta hanyar waya.A nan ko wace rana yana jin zafin nama da 'yan sa kai suke nunawa.

Ya ce, 'da wuya zan manta da ko wace rana da na ke aiki a wannan wuri,da akwai tsofaffi maza da mata da shekarunsu ya wuce saba'in kamar kakani suna neman yin rajista,sai mu lallashi su da rishin yarda shigarsu cikin ayyukan sa kai.duk da haka sun nuna wani hali na rashin son kai da bauta wa jama'a,su gamsu da aikin da za su yi.'

A hakika,ko ma'aikata ko 'yan sa kai dukkansu suna cike da kuzari suna aikin tukuru kan ayyukan da aka danka musu suna share fage ga wasannin Olympics na Beijing na shekara ta 2008 da shirin ba da taimakonsu yadda za a bukata.


1 2 3