Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-11 19:01:08    
Akwai wani shagon sayar da kayayyakin fasaha da aka yi da hannu a nan Beijing (1)

cri

Al'ummar kasar Sin kan kira kayayyakin dinki irin na Beijing da kayayyakin lu'ulu'un jade da aka sassaka da kuma kayayyakin da aka shafa musu fenti kwanciyoyi da yawa tukuna, daga baya an sassaka fenti din da sauran kayayyakin fasaha 5 da aka taba amfani da su a fadar sarakuna 'kyawawan kayayyakin fasaha mafi nagarta da aka taba amfani da su a fadar sarakuna', a ciki kuma tarihin kayayyakin fenti ya fi tsawo. Bisa bayanan da abin ya shafa, an ce, fasahar sassaka fenti irin na Beijing na daya daga cikin fasahohin fenti, ta gwanance a fannin sassaka. Da farko, masu fasaha sun shafa fenti kwanciyoyi gomai har ma daruruwa a kan abubuwa masu siffofi daban daban, zurfin fenti din ya kai milimita 15 zuwa 25, daga baya sun sassaka fenti din da wuka. A can da, jajaye da kwarran kayayyakin fenti sun sami rinjaye a cikin dukkan kayayyakin fenti.

Fentin da ake amfani da shi irin na halitta ne babu guba a ciki, ba ya kawo illa ga lafiyar mutane, haka kuma a kan yi amfani da shi tamkar magani ko kuma abinci. Irin wannan fenti na kan jure zaizayewa da zafi, na kan gudu daga tsutsotsi, shi ya sa kayayyakin fenti ba zai rube ba har dogon lokaci.

Kayayyakin fenti ya jawo sha'awar sarakuna sosai saboda amfaninsu da kyan ganinsu. Dimbin kasashen duniya sun mayar da kayayyakin fenti tamkar dukiya mai daraja ko kuma abin kyauta da suke bai wa baki masu girmamawa.(Tasallah)


1 2 3