Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-11 19:01:08    
Akwai wani shagon sayar da kayayyakin fasaha da aka yi da hannu a nan Beijing (1)

cri

Yanzu ana nuna kayayakin fasaha na gargajiya da aka taba amfani da su a fadar sarakuna iri-iri fiye da goma a shagon Baigongfang. Kayayyakin dinki irin na birnin Beijing wata alama ce ta wadannan kayayyakin fasaha na gargajiya, wadanda sai sarakuna kawai suke iya amfani da su a zamanin da. A bene na farko na shagon Baigongfang a hagu, akwai wani kantin sayar da kayayyakin dinki irin na Beijing.

Akwai samfurori da tsarin kayayyakin dinki irin na Bejing daban daban, sa'an nan kuma, kada a yi amfani da wasu zane-zanen da aka dinka a tufafi, sai wasu mutanen musamman, kamar su tufafin sarki da aka dinka dodo irin na kasar Sin wato dragon a Turance a kai da kuma watin da aka rubuta umurnin sarki a kansa.

An ce, a kan kammala dinka irin wannan kayan dinki na Beijing ne bisa matakai fiye da 10. Tun daga farko har zuwa karshe, mutum daya ne yake yin wannan aiki da kansa kawai. Saboda kyawawan zane-zanen da aka dinka, da nagartacciyar fasahar dinki tare da zare masu launuka daban daban da kuma al'ada mai zurfi na wannnan fasaha, har kullum dimbin masu yawon shakatawa na gida da na waje suna sha'awar ajiye kayayyakin dinki irin na Beijing.

Baya ga kayayyakin dinki na Beijing, bari mu kara saninmu kan wata fasaha daban da ake amfani da ita a fadar sarki, wato fasahar sassaka lu'ulu'un jade. An gaji fasahar sassaka lu'ulu'un jade irin na Beijing daga fadar sarki, shi ya sa kayayyakin lu'ulu'un jade da aka sassaka bisa wannan fasaha na da kyan gani, haka kuma suna nuna martabar sarauta.

Malam Yang Baozhong, wani kwararre ne da ya yi shekaru fiye da 30 yana aikin sassaka kayayyakin lu'ulu'un jade, ya gaya mana cewa,

'Fito da wani kyakkyawan kayan lu'ulu'un jade na dogara da fannoni 3, wato lu'ulu'un jade mai inganci da yin masa tsari mai kyau da kuma sassaka shi yadda ya kamata a tsanake. Duk wadannan abubuwa 3 ba a iya rasa daya daga cikinsu ba.'


1 2 3