A nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, akwai wani dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya irin na musamman, wato wani shagon sayar da kayayyakin fasaha da aka yi da hannu. Yau ma bari in yi muku karin bayani kan kayayyakin fasaha da aka taba amfani da su a fadar sarakuna, yanzu ana nuna su a shagon sayar da kayayyakin fasaha da aka yi da hannu na Beijing.
Shagon sayar da kayayyakin fasaha da aka yi da hannu mai suna Baigongfang yana kudancin birnin Beijing. A cikin babban zaure mai fadin kusan murabba'in mita dubu 50, yana kasancewa da ofisoshi fiye da 30 da kwararru suke bude. An raba kayayyakin fasaha na gargajiya da ake ajiye a cikin wadannan ofisoshin kwararru zuwa kashi 2, wato wadanda aka taba amfani da su a fadar sarakuna, da kuma wadanda fararen hula kan amfani da su. Bayan da ya ziyarci shagon Baigongfang, shugaba Eric Duluc na hadaddiyar kungiyar harkokin yawon shakatawa ta kasa da kasa ya yaba wa wannan shago sosai, ya mayar da shi tamkar fadar nune-nunen kayayyakin gargajiya ta Louvre ta kasar Sin. Malam Tao Ye, wanda ke aiki a shagon, ya ce,
'A zahiri shagon Baigongfang dakin ajiye kayayyakin gargajiya ne irin na musamman da ya sha bamban da saura. A shagon, masu yawon shakatawa suna iya kallon kayayyakin fasaha da ake ajiyewa da su a wajen a karkashin shugabancin masu jagorantarsu, ko kuma suna iya kara fahimtar wadannan kayayyakin fasaha ta hanyar hotuna, amma a yawancin lokuta, kwararru ko kuma wadanda ke koyi daga wajensu suna nuna yadda suke samar da kayayyakin fasaha a nan, ta haka masu yawon shakatawa suna iya yin mu'amala da kwararrun kai tsaye. Kwararrun suna yin kayayyakin fasaha a idanun masu yawon shakatawa, su kan amsa tambayoyin da ke jawo hankulan masu yawon shakatawa a ko wane lokaci.'
1 2 3
|