Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 15:29:09    
An shirya nune-nunen amfanin gona masu inganci na Taiwan a babban yankin kasar Sin

cri

A cikin shekarun nan da suka wuce, bankin shigi da fici na kasar Sin ya ba da babban taimako wajen inganta hadin kai a tsakanin bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan a fannin tattalin arziki da cinikayya. Malam Li Jun na bankin ya bayyana cewa, nan gaba bankin zai ci gaba da yin hadima ga 'yan kasuwa na Taiwan a fannin aikin noma. Ya ce, "bankinmu zai ci gaba da ba da taimakon kudi ga kungiyoyin tattalin arziki masu samar da amfanin gona na Taiwan da kamfanonin aikin noma da ake zuba musu jari cikin hadin guwia da kuma kasuwannin kudi na aikin noma."

Masu aikin noma na bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan sun nuna cewa, nune-nunen amfanin gona masu inganci na Taiwan da aka shirya a wannan gami, babban mataki ne da aka dauka don sa kaimi ga kara sayar da amfanin gona na Taiwan a babban yankin kasar, ta yadda za a kara inganta hadin kan bangarorin biyu a fannin aikin noma. (Halilu)


1 2 3