Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 15:29:09    
An shirya nune-nunen amfanin gona masu inganci na Taiwan a babban yankin kasar Sin

cri

Amfanin gona da aka nuna a gun nune-nunen sun hada da 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu da shinkafa da shayi da albarkatun teku da sauran iri-iri da yawansu ya wuce 400. Duk wadannan amfanin gona sun sami karbuwa sosai daga wajen mazaunan biranen daban daban. Malam Zhang Yongcheng, babban direktan kungiyar manoma ta Taiwan ya bayyana cewa, a sakamakon nasarar da aka samu wajen shirya wadannan nune-nune, amfanin gona na Taiwan sun kara shahara a babban yankin kasar Sin. Ya kara da cewa, "ta hanyar nune-nunen, 'yan biranen sun ga amfanin gona masu inganci iri iri na Taiwan sosai, da amfanin gona da 'yan kasuwa na Taiwan da ke a babban yankin kasar ke samu. Muna fatan za a ci gaba da shirya irin wadannan nune-nune a nan gaba, muna maraba da mazaunan birane da su ziyarci nune-nunen, ta yadda manoma na Taiwan za su bayyana musu abubuwa a kan amfanin gona na Taiwan."

Wani jami'in ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin ya ce, Taiwan yana da kyawawan ire-iren amfanin gona, da fasahar aikin noma ta zamani, da tsarin kasuwannin sayar da amfanin gona zuwa kasashen waje da sauransu. Babban yankin kasar Sin kuma yana da albarkatun kasa masu arziki, da kyawawan manyan ayyuka da sauransu. Don haka idan bangarorin biyu sun inganta hadin kansu a fannin aikin noma, za su iya kyautata tsarin aikin nomansu, su taimaka wa juna, su sami nasara tare.


1 2 3