Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 15:29:09    
An shirya nune-nunen amfanin gona masu inganci na Taiwan a babban yankin kasar Sin

cri

A karshen watan Yuli da ya wuce, kungiyar musanyar aikin noma ta bangarori biyu na mashigin teku na Taiwan da kungiyar manoma ta lardin Taiwan na kasar Sin sun hada kansu sun shirya "nune-nunen amfanin gona masu inganci na Taiwan na shekarar 2007" a birane da dama na babban yankin kasar Sin. Ta hanyar nune-nunen, amfanin gona masu inganci na Taiwan sun kara samu karbuwa daga wajen jama'ar babban yankin kasar, kuma an kara sa kaimi ga yin musanya da hadin kai a tsakanin bangarorin biyu a fannin aikin noma.

Tun daga ran 20 zuwa ran 25 ga watan Yuli da ya wuce, bi da bi aka shirya nune-nunen amfanin gona masu inganci na Taiwan a biranen babban yankin guda shida kamar Shanghai da Nanjing da Fuzhou da Wuhan da Guangzhou da kuma Dalian. Kungiyar manoma ta lardin Taiwan da kungiyoyin manoma na gundumomi da kauyuka da kamfanonin amfanin gona da yawa na lardin sun shiga nune-nunen don gwada wa jama'ar babban yankin amfanin gona masu inganci na Taiwan.

Malam Chen Zhiwei wanda ya fito daga gundumar Nantou na Taiwan ya bayyana cewa, daidai kamar yadda wakilan 'yan kasuwa na Taiwan suke yi ne, shi ma yana fatan zai iya fadada hanyar da yake bi wajen sayar da amfanin gona a babban yankin kasar ta hanyar nune-nunen. Ya kara da cewa, "mun zo nan ne domin neman samun damar kasuwanci, muna son samun damar hadin kanmu da babban yankin kasar ta hanyar nune-nunen nan."


1 2 3