
A ran 3 ga watan Satumban da muke ciki, Ban Ki-moon ya isa birnin Khartoum, ya bayar da wani jawabi mai lakabi "Gudummowar da M.D.D. take bayar lokacin da duniya take samun sauye-sauye", inda ya bayyana cewa, ya kamata a daidaita batun Darfur ta hanyoyin shimfida zaman lafiya da ciyar da ayyukan siyasa gaba da samar da taimakon jin kai da neman bunkasuwa a shiyyar.
Amma a waje daya, manazarta sun nuna cewa, ba a iya yin watsi da sabane-sabanen da ke kasancewa a tsakanin Sudan da M.D.D. ta wannan ziyara daya kadai da Ban Ki-moon ya yi a kasar Sudan ba. A cikin halin da ake ciki yanzu, ba zai yiyuwa ba ne ta yarda da M.D.D. ta maye gurbin ba da jagoranci na kungiyar Tarayyar Afirka kan batun Darfur. (Sanusi Chen) 1 2 3
|