Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-10 14:23:48    
Ziyarar da Ban Ki-moon ya yi a kasar Sudan ta kyautata amfanin MDD kan batun Darfur

cri

Babi na 3 na wannan sanarwa yana kunshe da matakan da M.D.D. za ta dauka domin taimakawa kasar Sudan wajen tabbatar da zaman lafiya da neman cigaba a kasar. Manazarta na wurin suna ganin cewa, sanyan abubuwa game da kokarin farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya a Darfur a cikin wannan babi na 3 yana da ma'anar musamman, wato yana almantar cewa, gwamnatin kasar Sudan tana son ganin karin gudummowar da M.D.D. za ta iya bayarwa kan batun Darfur. Sabo da dalilai iri iri, a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, huldar da ke tsakanin kasar Sudan da M.D.D. ta shiga cikin mawuyacin hali.

A watan Yuni na shekarar da muke ciki, Ban Ki-moon, babban sakataren M.D.D. ya bayar da wani bayani a kan jaridar Washington Post ta kasar Amurka, inda ya nuna cewa, dalilan da suka sanya tashin hankali a shiyyar Darfur su ne karancin ruwa da sauran albarkatun halittu a sakamakon dumamar yanayin duniya da gurbatar muhallin shiyyar Darfur. Sakamakon haka, an ta da tashin hankali a tsakanin kabilun makiyaya da kabilun manoma na wurin domin neman yankuna da yankunan da ke da ruwa. Kafofin watsa labaru na kasashen duniya sun yi amfani da wannan bayani har sau da yawa, ya kuma jawo hankulan mutane sosai. Kasar Sudan ma ta fara jin dadin wannan bayanin da Mr. Ban Ki-moon ya rubuta domin yana mai da hankali kan batun Darfur bisa hakikanin halin da ake ciki a shiyyar Darfur. Sabo da haka, shugaba Bashir na Sudan ya gayyaci Ban Ki-moon da ya kai wa kasar Sudan ziyara domin kyautatawa da karfafa huldar da ke tsakanin Sudan da M.D.D. Bugu da kari kuma, a watan Yuni na shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa ta yarda da a girke rundunar sojan hadin guiwa ta M.D.D. da ta kungiyar Tarayyar Afirka a shiyyar Darfur, kuma ta amince da kudurin girke rundunar sojan hadin guiwa ta M.D.D. da ta AU a shiyyar Darfur da aka zartas da ita a karshen watan Yulin da ya gabata. A ganin Ban Ki-moon lokaci ya yi da ya kai ziyara a kasar Sudan.


1 2 3