
A ran 6 ga wata, Mr. Ban Ki-moon, babban sakataren M.D.D. da shugaban kasar Sudan Omar Hassan Ahmed Al-Bashir sun bayar da wata hadaddiyar sanarwa a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan, inda suka sanar da cewa, gwamnatin Sudan da kungiyoyin da ke shiyyar Darfur wadanda suke adawa da gwamnatin Sudan za su farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar Libya a ran 27 ga watan Oktoba. Wannan ya almantar cewa, ziyarar da Mr. Ban Ki-moon ya yi a kasar Sudan ta samu nasara, kuma ta bayyana cewa, yanzu M.D.D. ta sake taka muhimmiyar rawa kan batun Darfur.
Wannan hadaddiyar sanarwar ta kunshi babi 3. A cikin babi na farko, an jaddada cewa, gwamnatin kasar Sudan da M.D.D. dukkansu suna ganin cewa, ziyarar da Mr. Ban Ki-moon ya yi a kasar Sudan tana da muhimmanci sosai. Za ta yi wa bangarorin biyu amfani wajen karfafa huldar abokantaka da ke tsakaninsu domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaba. Ana kuma raya irin wannan hulda ne a tsakaninsu bisa ka'idojin girmamawa ikon mulkin kasar Sudan cikin 'yanci da cikakkun yankuna da dinkuwar duk kasar Sudan gaba daya da M.D.D. take yi. A cikin babi na biyu, gwamnatin kasar Sudan ta bayyana cewa, za su kara yin hadin guiwa domin farfado da sabon zagaye na shawarwarin shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur da girke hadaddun rundunonin sojojin gaurayyar M.D.D. da kungiyar Tarayyar Afirka domin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur.
1 2 3
|