Jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkoki da kanta da ke a arewa maso yammacin kasar Sin jiha ce mafi girma a kasar. A gun irin wannan bikin baje koli da aka shirya a wannan gami, jihar ta nuna samfurorin injunan samar da wutar lantarki masu aiki da karfin iska, da sakamako da aka samu wajen binciken abubuwa masu rai da na'urori iri daban daban. Malam Ma Bing, mataimakin shugaban sashen kimiyya da fasaha na babban kamfani mai suna Zhonghe na jihar Xinjiang ya bayyana cewa, "a shekarar nan, mun zo da sabbin ayyuka biyu na yin kayayyakin electron, Manufar kamfaninmu ita ce bunkasa sabbin kayayyakin electron. Muna binciken abubuwa ne wadanda ya zuwa yanzu ba a yi shi a gida ba, muna neman fitar da abubuwa da ba a iya yi su yanzu a kasar."
Kwararru sun bayyana cewa, bikin baje kolin kimiyya da fasaha na kasa da kasa na Beijing ya samar da kyakkyawar hanya da jihohin yammacin kasar Sin ke bi wajen yin musanya da hadin kai a tsakanin da kasashen waje. Yanzu, jihohin sun riga sun sami kyakkyawan sakamako wajen yin hadin kai a tsakaninsu da sauran jihohin kasar da kuma kasashen waje don bunkaa harkokin tattalin arziki da kimiyya da fasaha. Wadannan sakamako za su yi taka rawa sosai wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da kimiyya da fasaha a jihohin nan.(Halilu) 1 2 3
|