Bikin baje kolin kimiyya da fasaha na kasa da kasa wanda a kan shirya dau daya a ko wace shekara a Beijing, babban birnin kasar Sin, ba ma kawai ya zama nunin sabbin sakamako da masana'antun zamani na gida da waje ke samu a fannin kimiyya da fasaha ba, har ma ya zama hanyar da jihohin yammacin kasar Sin ke bi wajen gwada albarkatunsu masu rinjaye da neman jawo kudaden jari. A gun bikin baje kolin da aka shirya a karo na 10 a birnin Beijing ba da dadewa ba, wakilan jihohin yammacin kasar sun nuna sabbin sakamako da suka samu a fannin kimiyya da fasaha, kuma sun ba da muhimmanci sosai ga inganta hadin kai da musanya a tsakaninsu da masana'antun gida da na waje.
Kungiyoyin wakilan kasashe da shiyyoyi sama da 30 da masana'antun gida da waje da yawansu ya kai kusan 2,000 sun halarci bikin baje kolin da aka shirya a karo na 10 a birnin Beijing. Malam Xu Shoucheng, gwamnan jihar Gansu da ke yammacin kasar Sin ya halarci bikin baje kolin don gabatar da ayyukan tattalin arziki da za a yi a jihar. Ya ce, "jiharmu tana ba da muhimmanci sosai ga bikin baje kolin da ake shiryawa a birnin Beijing. Jiharmu da ke bakin iyakar kasa ta yi baya-baya idan an kwatanta ta da Beijing da sauran jihohi na kasar a fannin aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude wa kasashen waje kofa da raya kasuwanni. Sabo da haka gwamnatin jiharmu ta yanke shawara kan gabatar da jiharmu ta hanyar bikin baje kolin don aminanmu na gida da waje za su kara fahimtar jiharmu, ta yadda za mu gina jihar Gansu tare."
1 2 3
|