Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-31 15:28:47    
Jihohin yammacin kasar Sin ke neman inganta hadin kai ta hanyar bikin baje kolin kimiyya da fasaha na kasa da kasa na Beijing

cri

Jihar Gansu ta fara halartar bikin baje kolin ne a shekarar 2,000. Ya zuwa yanzu, yawan kasashe da shiyyoyi da suka kulla huldar hadin kai a tsakaninsu da jihar a fannin tattalin arziki da cinikayya ya kai kusan 130. An cim ma yarjejeniyoyi 32 game da yin ayyuka a jihar ta hanyar bikin baje kolin. Aiwatar da yarjejeniyoyin na ba da babban taimako wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar Gansu.

A gun bikin baje kolin kimiyya da fasaha na kasa da kasa na Beijing da aka shirya a karo na 10, jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon aiwatar da harkokin kanta da ke a kudu maso yammacin kasar Sin ta nuna shayi da abubuwa masu gina jiki da lu'ulu'u da sauransu wadanda suka jawo hankulam maziyarta masu dimbin yawa. Malam Ou Qizhen, babban manajan kamfanin lu'u'lu'u mai suna Yongming na birnin Nanning na jihar Guangxi wanda ya halarci bikin baje kolin ya yi takama da cewa, "mun nuna lu'ulu'u mafi kyau a duniya a gun bikin baje kolin. Masu saya da suka yi odar lu'ulu'u sun yi yawa. Lalle, mun riga mun sami kyakkyawan sakamako a gun bikin, haka kuma akwai masaya da yawa wadanda ke shirin tattaunawa da mu a kan cinikayyar lu'ulu'u."


1 2 3