Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-30 15:57:43    
Kasar Sin ta fara gyara tsarin ka'idojin bunkasa kimiyya da fasaha

cri

Domin karfafa kwarin gwiwa wajen yin kirkira cikin yanci,daftarin shiri ya kuma tanadi tsarin saye na gwamnati yadda ya dace,haka kuma ya tanadi sabon tsarin bincike da nazarin fasahohin da aka shigo da su daga kasashen ketare,da kuma kara nakalta da sabunta su.

Domin karfafa kwarin gwiwar masana'antu wajen yin kirkira cikin 'yanci da inganta matsayinsu na ginshikai wajen kirkira,an kara babi dake da lakabi haka "ci gaban masana'antu a fannin fasahohi a cikin daftarin shiri.Ciki har da gwamnatin ta girka asusun musamman da kudin gwamnati da ba da rancen kudi tare da ragen ruwan kudi da tabbaci ga masana'antu wajen yin kirkira cikin yanci da kuma amfani da sakamakon da suka samu.Gwamnatin ta kafa kasuwar jari da bunkasa ta domin gaggauta kirkira cikin yanci da nuna musu goyon baya da su shiga kasuwar hannayen jari.

Kirkiro sabbi a fannin kimiyya da fasaha na bukatar zubar jari da karin amfanin jarin da aka zuba a fannin kimiyya da fasaha. Kan batun nan Mr Wan Gang ya bayyana cewa "Daftarin shirin ya tanadi cewa kamata ya yi gwamnatin ta rika zuba jarin da ake bukata a fannin kimiyya da fasaha,karin kudin da ake amfani a fannin kimiyya da fasaha ya fi karin kudin kashewa na yau da kullum yawa na shekara daya.gwamnatin ta kafa wani tsarin daidaituwa,ta kafa wani tsarin da ya hada hukumomin bincike da na yin gwaje-gwaje,da shimfida wani tsari na kowa ke iya amfani da na'urorin binciken kimiyya."(Ali)


1 2 3