Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-30 15:57:43    
Kasar Sin ta fara gyara tsarin ka'idojin bunkasa kimiyya da fasaha

cri

Kwanan baya karo na farko ne da kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya zartas da wani daftarin shirin bunkasa kimiyya da fasaha na kasar Sin bayan da aka yi shekaru uku ana nazarin daftari da kuma kyautata shi.A cikin daftarin shiri a fili ne an kara bayyana nauyin da ke bisa wuyan gwamnati da daidaita albarkatan kimiyya da fasaha da kara kudin da za a zuba a wajen bunkasa kimiyya da fasaha,da gaggauta mai da masana'antun sabbin ginshikai wajen sabunta fasahohi.

Tsarin ka'idojin bunkasa kimiyya da fasaha da ake amfani da shi cikin shekaru 14 da suka gabata ya taka muhimmiyar rawa wajen kara bunkasa kimiyya da fasaha na kasar Sin.Duk da haka,tare da cigaban tattalin arziki da zamantakewa,kasar Sin tana fuskantar matsalolin da ake bukata a daidaita su cikin gaggawa a fannin kimiyya da fasaha.kamar su masana'antu ba su nuna kwazo da himma a fannin kimiya da fasaha ba,ba su kara kudin da ake bukata a wannan fanni ba,haka kuma masana kimiyya da fasaha suna bukatar karin kwarewarsu,da rashin amfani da sakamakon da aka samu daga wajen binciken ilimin kimiyya da fasahohi.A sa'I daya kuma an samu sauye sauye wajen bunkasa ilimin kimiyya da fasaha a kasar Sin,an fitar da muhimman manufofi na bunkasa kimiyya da fasaha,da daukar matakai da kawo sauyi a wannan fannin,"sabunta fasahohi cikin yanci da neman samun babban cigaba a wasu sassa da samu madogara ga cigaba da nuna alkibla" ya zama ka'idar jagora ga kasar Sin a sabon zamani wajen bunkasa kimiyya da fasaha.An mai da gina kasar Sin ta zama kasa ta sabo ful wajen kirkira a shekara ta 2020 burin bunkasuwa.Bisa wannan halin da ake ciki,tsarin bunkasa kimiyya da fasaha da ake amfani da shi bai iya biyan bukatun cigaban da ke akwai ba.


1 2 3