Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-30 15:57:43    
Kasar Sin ta fara gyara tsarin ka'idojin bunkasa kimiyya da fasaha

cri

A gun taron kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi kwanan baya,ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Mr Wan Gang ya yi bayani kan tsarin bunkasa kimiyya da fasaha da aka yi masa kwaskwarima da cewa "Domin warware matsalolin da ake akwai a fannin manufofi da bayyana muhimmin shirin da manufofin da ake bi a fili ta shari'a domin bunkasa kimiyya da fasaha,abin da ya zama wajaba a gyara tsarin ka'idojin bunkasas kimiyya da fasaha."

Tsarin ka'idojin bunkasa kimiyya da fasaha yana da muhimmancin gaske a fannin kimiyya da fasaha kamar manyan dokoki a kasa.sabili da haka an rubuta "gina wata kasa mai kirkira ta sabo ful a cikin daftarin shiri,wannan babban ci gaba ne da aka samu a ganin mutane waje da fannin nan.A cikin daftarin shiri,an karfafa gwiwar masu yin kirkira cikin yanci.Domin karfafa kwarin gwiwar wadanda ke da tunanin kirkira su dauki nauyi a ayyukan asusun kimiyya da fasaha da ayyukan shirye shiryen kimiyya da fasaha,daftarin shirin ya tanadi cewa kamata ya yi a baiwa mallakar ilimin kirkiro ga wadanda suka dauka nauyi kan ayyukan kimiyya da fasaha.Kan batun nan Mr Wan Gang ya yi bayani da cewa"Ayyukan asusun kimiyya da fasaha na gwamnati ko ayyukan shirye-shiryen kimiyya da fasaha sun samar da ikon mallakar ilimin kirkiro wanda ya shafi harkokin tsaron kasa da zaman lafiya da moriyar jama'a a zamantakewa,ya kamata gwamnati ta mallake shi, ikon mallakar ilimin kirkiro na sauran fannoni kuwa an baiwa wadanda suka dauka nauyi,wadanda suka samu mallakar ilimin kirkiro za su iya amfani da shi bisa doka.gwamnatin kasa na iya amfani da shi domin biyan bukatun gwamnati da na jama'a masu dimbin yawan gaske."

Ban da wannan kuma, domin karfafa kwarin gwiwa ga masana kimiyya da fasaha,a cikin daftarin shiri,an tanadi cewa kan ayyukan binciken kimiyya dake yiwuwar hasara,in akwai shaidar da ta tabbatar da masana kimiyya da fasaha da suka dauka nauyin binciken sun cika alhakkin da wuyansu cikin tsanaki, amma ba su cimma burinsu ba ,za su iya kammala ayyukansu.Wannan ya jawo hankulan masana kimiyya da fasaha da cewa tsarin ne na gafara da hassara.


1 2 3