Shayin Wuliqing na daya daga cikin ganyayen shayi masu daraja da aka samu a babban tsaunin Xianyu kawai. Saboda babban tsaunin Xianyu na cikin gajimare a duk shekara, shi ya sa ake kiran ganyayen shayi da aka samu a nan 'Wuliqing', wato ganyayen shayi da suka girma cikin gajimare. Bisa abubuwan da ke cikin tsoffin littattafai, an ce, an fara shuka bishiyoyin shayi a babban tsaunin Xianyu tun daga shekarar 300 kafin haihuwar Annabi Isa A.S.. Ana samar da ganyayen shayi ire-ire da yawa a babban tsaunin Xianyu, baya ga shayin Wuliqing, jan shayi da ake samarwa a gundumar Qimen na lardin Anhui su ma sun shahara a gida da kuma a ketare.
Ya zuwa yanzu dai a babban tsaunin Xianyu, ana yin amfani da ganyayen da suka fado da kuma rassan bishiyoyi da suka mutu tamkar taki wajen shuka bishiyoyin shayi, a maimakon takin zamani. Ban da wannan kuma, ana soya ganyayen shayi ta hanyar da aka saba bi yau da dubban shekaru da suka wuce. Shanyin da aka samu daga babban tsaunin Xianyu na da kamshi mai sigar musamman, haka kuma cike yake da sinadari masu amfanin lafiyar mutane.
A babban tsaunin Xianyu, kungurmin daji da ba a taba yin amfani da shi ba da ke wuri mai tsayin mita dubu daga leburin teku, da dimbin bishiyoyin shayin Wuliqing masu dogon tarihi, da kuma lambunan bishiyoyin shayi da aka bude wa masu yawon shakatawa na gida da na waje sun fi jawo hankulan masu yawon shakatawa. A shekarar 2005, jirgin ruwa na Gotheborg da aka kera ta hanyar gargajiya ya sake zuwa kasar Sin daga Sweden ta hanyar da aka bi yau da daruruwan shekaru da suka gabata, ma'aikatan jirgin ruwan sun ziyarci babban tsaunin Xianyu. A cikin lambunan bishiyoyin shayi, ma'aikacin jirgin ruwan malam Max Larsson da sauran ma'aikatan sun ajiye ganyayen shayi na Wuliqing mai dogon tarihi da suka tsamo daga teku a hannunsu, sun kalli danyun ganyayen shayi da ke bishiyoyin, sun ji zumudi sosai. Malam Larsson ya ce,
'A halin yanzu dai, mutane na yin ayyukan gona ta hanyar gargajiya, sun gaji irin wannan hanya daga kaka da kakanninsu kawai. Yanzu ina cikin irin wannan tsohon lambun bishiyoyin shayi, na ji shekaru fiye da dari 3 sun wuce a idona. Na nuna halin karimci, ina nuna girmamawa ga dukkan abubuwan da nake gani a wajen.'
Bayan karni guda 3, ganyayen shayi na Wuliqing sun dawo gida. Ta hanyar musamman ne 'yan kasuwa masu sayar da ganyayen shayi da suka zo daga babban tsaunin Xianyu suka yi maraba da bakinsu na Sweden da suka maido da ganyayen shayi masu dogon tarihi a gida. Sun bai wa sabon jirgin ruwa na Gotheborg danyun ganyayen shayi na Wuliqing. A kan ko wane gwangwanin fadi-ka-mutu mai cike da ganyayen shayi, akwai alamar siffar jirgin ruwa na Gotheborg. Madam Liu Guoqing, mataimakiyar magajin garin Chizhou, ta ce,
'Ina fari ciki saboda sanin cewa, an tsamo ganyayen shayi na babban tsauninmu daga tsohon jirgin ruwa na Gotheborg. Na yi matukar mamaki domin ganin wadannan tsoffin ganyayen shayi.'
1 2 3
|