Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-28 15:36:23    
Shan shayi a babban tsaunin Xianyu

cri

Babban tsaunin Xianyu da ke birnin Chizhou na lardin Anhui a tsakiyar kasar Sin ya shahara ne saboda kyan karkara da kuma samar da mashahuran ganyayen shayi daban daban a tarihi. A cikin shirinmu na yau, zan jagoranci ku zuwa Anhui domin kai ziyara a babban tsaunin Xianyu da kuma shan shayi a wajen.

A shekarar 1745, a kan hanyarsa zuwa komawa mahaifiyarsa kasar Sweden daga kasar Sin, wani jirgin ruwa na kasuwanci mai suna Gotheborg ya nutse a sakamakon yin karo da dutsen teku. A shekarar 1986, an soma tsamo kayayyakin da aka yi jigilarsu a kan jirgin ruwa na Gotheborg daga teku. Mutane sun yi mamaki sosai saboda ganin cewa, a cikin wadannan kayayayki, ya zuwa yanzu dai an iya shan koren shayi irin na kasar Sin da ke cikin ruwan teku har na tsawon shekaru 200 ko fiye, yana da kamshi sosai. Wadannan ganyayen shayi sun hada da mashahurin shayin Wuliqing mai dogon tarihi da aka samu daga babban tsaunin Xianyu na lardin Anhui. Malam Max Larsson, dan kasar Sweden, wanda ya taba shiga ayyukan tsamo jirgin ruwa na Gotheborg daga teku, ya waiwayi abubuwan da suka wakana a lokacin can, ya kasance lokaci ya koma baya. Ya ce,

'Mun gano tsoffin ganyayen shayi irin na kasar Sin ton 370 daga tarkacen jirgin ruwa na Gotheborg. An ajiye kwalaban tangaran da ke cike da ganyayen shayi a cikin akwatunan katako. Wata rana da dare, mun shirya wani biki don shan shayin da muka tsamo, shayin nan na da dadin sha kwarai, har ma ban iya sifanta ba.'


1 2 3