Dadin dadawa kuma, a zahiri, gwamnatin Iraq mai ci ba ta iya yin watsi da goyon baya da tallafi daga sojojin Amurka ba a harkokin tsaron kai, amma duk da haka, kasancewar aikin soja a Iraq da kuma tsoma baki cikin harkokin gida da na waje na Iraq da rundunar sojan Amurka ke yi sun kawo babbar illa ga gwamnatin Maliki da sojojin Iraq wajen bunkasa kansu. A fannin aikin soja, mamayewar Iraq da sojan Amurka ke yi cikin dogon lokaci ya raunana kwarin gwiwar 'yan sanda da sojojin tsaron Iraq, 'yan ta'adda sun kutsa kai cikin rundunar 'yan sanda cikin dogon lokaci. A fannin harkokin gida, kasancewar aikin soja na Amurka a Iraq ta sa gwamnatin Maliki ta yafe wa tsohuwar gwamnatin da tsoffin sojoji da lallashin 'yan tsaka-tsaki da kuma mayar da dakarun dake adawa da Amurka saniyar ware, ta haka, gwamnatin Iraq ba ta sami babban ci gaba wajen tabbatar da sulhuntawa ta fuskar siyasa ba. A fannin harkokin waje kuma, Mr. Maliki yana fatan za a kyautata dangantakar da ke tsakanin kasarsa da kasashen da ke makwabtaka da Iraq, kamar su kasashen Iran da Syria, ta haka wadannan kasashe za su taka rawa a fannonin tabbatar da tsaron kai da farfado da tattalin arziki da samun sulhuntawa ta fuskar siyasa a Iraq. Amma gwmanatin Bush ta sha kawo cikas ga kokarin da gwamnmatin Maliki ke yi a harkokin waje, ta yadda Mr. Maliki ya shiga halin kaka-ni-kayi a harkokin waje.
Bisa halin da ake ciki a gajeren lokaci, gwamnatin Maliki za ta ci gaba da dogara da Amurka, a sa'i daya kuma, yana kasancewa da matsaloli a tsakaninsu. Amma duk da haka, saboda tsanancewar gwagwarmaya a tsakanin jam'iyyu 2 a Amurka, gwamnatin Bush za ta kara fuskantar matsin lambar siyasa a gida, tabbas ne gwamnatin Maliki za ta fuskanci mawuyancin hali a harkokin gida da na waje.(Tasallah) 1 2 3
|