Ran 26 ga wata, a gun wani taron manema labaru da aka yi, firayim minista Nouri al-Maliki na kasar Iraq ya yi suka ga madam Hillary Clinton, 'yar majalisar dattawa ta kasar Amurka kuma 'yar jam'iyyar Dimokuradiyya ta kasar da kuma Carl Levin, shugaban kwamitin aikin soja na majalisar dattawa ta Amurka saboda sun mayar da Iraq tamkar wani bangare na Amurka, suna kuma tsoma baki cikin harkokin gida na Iraq sosai. Ya yi kira ga wadannan manyan jami'an siyasa na Amurka da su girmama Iraq a yayin da suke magana kan Iraq.
Akasarin ra'ayoyin jama'a na ganin cewa, kafin majalisar dokokin Amurka ta maido da aikinta a ran 4 ga watan Satumba, David Petraeus, kwamandan koli na sojan Amurka a Iraq da Ryan Crocker, jadakan Amurka a Iraq za su tashi zuwa birnin Washington na Amurka, sa'an nan kuma, Amurka za ta gabatar da rahoton kimanta halin da Iraq ke ciki bayan tura karin sojoji dubu 30 zuwa wannan kasa, wannan matakin da Mr. Maliki ya dauka, wanda ba safai ya kan dauka ba, ya nuna damuwar Mr. Maliki kan sauye-sauyen da Amurka za ta yi wa manufofinta domin Iraq. Dalilai da yawa sun sa Mr. Maliki ya nuna irin wannan damuwa.
1 2 3
|