Kafin wannan kuma, baya ga sukan da 'yan majalisar dattawa ta Amurka kuma 'yan jam'iyyar Dimokuradiyya ta kasar suka kai musu ba, Mr. Maliki da gwamnatinsa sun sami zargi daga sauran manyan jami'an Amurka da suka hada da shugaba Bush. Ban da wannan kuma, bisa wani rahoton kimantawa da hukumar leken asiri ta Amurka ta bayar a kwanan baya, an ce, Iraq ba ta sami ci gaba a harkokin siyasa ba, haka kuma, ana nuna damuwa kan karfin gwamnatin Iraq wajen mulkin kasar. A cikin irin wannan hali ne, Mr. Maliki ya yi suka ga jam'iyyar Dimokuradiyya ta Amurka, a sa'i daya kuma, ya bayyana wa gwamnatin Bush burinsa cikin sahihanci, wato kada ta yi watsi da shi. A gun taron manema labaru da aka yi a ran 26 ga wata, Mr. Maliki ya ce, ya yi fatan cewa, a cikin rahoton kimantawa, Mr. Petraeus zai bayyana ra'ayinsa na goyon bayan gwamnatin Iraq, ta haka, za a iya bata ran wadannan 'yan siyasa da ke yunkurin yin amfani da wannan rahoto domin nuna kin yarda da gwamnatin Iraq.
Masu nazarin al'amuran yau da kullum sun nuna cewa, ko da yake Mr. Maliki ya nuna rashin gamsuwa sosai kan sukan da gwamnatin Bush da jam'iyyar Republican ta Amurka suka bayar, amma ya san cewa, yanzu bai iya yin watsi da goyon bayan da Amurka ke bayarwa ba. A gaskiya kuma, ya yi suka ga 'yan jam'iyyar Dimokuradiyya ne don nuna wa gwamnatin Bush cewa, in gwamnatin Bush ta canza manufofin Iraq cikin sauri saboda matsin lambar da 'yan jam'iyyar Dimokuradiyya ke bayarwa, to, gwamnatin Iraq za ta fada cikin mawuyacin hali, mai yiwuwa ne za a tsananta gwagwarmaya a tsakanin rukunonin siyasa daban daban na Iraq, Iraq kuwa za ta kara fuskantar baraka mai tsanani.
1 2 3
|