Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-17 17:54:05    
Takardar bayani kan ' Halin ingantaccen abinci na kasar Sin'

cri

A cikin takardar bayanin, an jaddada cewa, a cikin shekaru da dama da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta dukufa wajen sa ido kan ayyukan samar da ingantaccen abinci, wato ke nan ta kafa doka kan ingantaccen abinci da kuma kaddamar da ma'aunin bincike kan ayyukan samar da ingantaccen abinci ; Kazalika, gwamnatin kasar Sin ta yi musanye-musanye da hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya don tabbatar da ingancin abinci. Malam Luo ya kara da cewa : ' Lallai wannan takardar bayani ta dace da hakikanin halin da ake ciki yanzu a kasar Sin a game da ingancin abinci.'

Alkaluman da aka bayar cikin wannan takardar bayani na nuna cewar, yawan kudin da kasar Sin ta samu daga shigi da ficin abinci a shekarar bara ya kai dolar Amurka biliyan 40, wato ke nan ya karu da kashi 21 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokaci na shekarar 2005. Cikin shekaru da dama da suka gabata, yawan cancantar abinci da kasar Sin take sayar wa kasashen waje, har kullum yana tsayawa kan matsayin sama da kashi 99 cikin kashi 100.


1 2 3