Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-17 17:54:05    
Takardar bayani kan ' Halin ingantaccen abinci na kasar Sin'

cri

Yau Jumma'a, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wata takardar bayani kan ' Halin ingantaccen abinci na kasar Sin', wadda ta nuna cewa, a galibi dai, matsayin ingancin abinci na kasar Sin yana ta daguwa, wato ke nan ana ta kyautata yanayin samar da ingantaccen abinci; kuma kasar Sin tana so ta sanya kokari matuka tare da sauran kasashe da yin mu'amala da hadin gwiwa tsakaninsu don sarrafa ayyukan samar da ingantaccen abinci da daukaka ci gaban yunkurin cinikayyar duk duniya.

Wakilinmu ya ziyarci Malam Luo Yunbo, kwararre a fannin kimiyyar abinci da abubuwa masu gina lafiyar jiki daga Jami'ar noma ta kasar Sin don jin ta bakinsa game da batun ingantaccen abinci, inda ya furta cewa, batun ingantaccen abinci ya fi janyo hankalin duk duniya. Gwamnatin kasar Sin ta fito da wannan takardar bayani ne domin samar wa masu saye-saye kyakkyawar hanyar samun labari dangane da ingantaccen abinci na kasar Sin, da kuma bayyana ra'ayinta na sauke nauyin dake bisa wuyanta na samar da ingantaccen abinci. Malam Luo Yunbo ya fadi cewa: 'Kasar Sin wata babbar kasa ce dake yin shigi da fici da sarrafe-sarrafen abinci, kuma wata babbar kasa ce mai sayen kayayyaki da kuma fitar da abinci zuwa ketare. Saboda haka, batun ingancin abinci ya janyo hankulan bangarori daban-daban'.


1 2 3