Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-16 16:04:56    
Rikici bai zo karshe ba bayan yakin Iraki

cri

Ban da wannan kuma gwamnatin kasar Iraki ba ta da kyakkyawar kwarewa wajen gudanar da harkokin kasar da kuma sarrafa hali mai tsanani da take ciki. Yakin Iraki ya karya tsohon tsarin mulkin kasar Iraki, da kuma rusa sojojin Iraki, sabo da haka zamantakewar al'ummar al'umma ta shiga halin yamutsi. Ko da yake kasar Amurka ta nuna goyon baya ga gwamnatocin Iraki bi da bi, amma dukkansu sun kasance cikin gajerren lokaci ne sakamakon rashin samun goyon baya daga dimbin mutane. Duk da yake an samu gwmanatin kasar Iraki ta yanzu ta hanyar zabe, amma kafuwar gwamnatin wani sakamako ne da rukunoni daban daban suka samu bayan da suka yi rangwame da juna. Ana kasancewar da rikice-rikice daban daban a cikin gwamnatin, shi ya sa aka lallata kwarewarta wajen gudanar da harkokin kasar. Yanzu gwamnatin kasar Iraki da ke karkarshin jagorancin Nuri Al-Maliki tana fuskantar matsalar durkushewa sakamakon janye jikin rukunin Sunnite da dai sauran rukunoni, shi ya sa ba ta iya sarrafa mummunen halin da ake ciki yanzu ba.

Bugu da kari kuma, an riga an tabbatar da cewa, dalilai biyu da suka sanya gwamnatin Bush ta afkawa Iraki da yaki ba su da sahihanci. Shi ya sa ko da yake kasar Amurka ta samu nasara ganin bayan Sadam, amma hakika rikici bai kare ba a Iraki. Ko da yake mamayewa da aka yi a kasar Iraki, da jibge dubban sojojin Amurka a kasar cikin dogon lokaci, da kuma yawan daukar matakan kai samame sun rage karfin dakaru masu adawa da Amurka bisa wani mataki, amma a waje daya kuma dubban fararen hula suka rasa rayukansu sakamakon wannan, shi ya sa dole ne suke kin jinin Amurka sosai. Masu lura da al'amuran duniya sun nuna cewa, kasar Iraki ba za ta samu kwanciyar hankali ba har sai sojojin Amurka sun janye daga kasar.(Kande Gao)


1 2 3